Iran Ta Ce Ta Harbo Jirgin Amurka Maras Matuki a Qeshm

Dakarun Juyin Juya Halin Iran (IRGC) sun ce sun harbo wani jirgin sama maras matuƙi kirar MQ-9 mallakin rundunar sojin Amurka a sararin samaniyar tsibirin Qeshm da ke kudancin Iran.

Sashen hulɗa da jama’a na IRGC ya bayyana cewa an harbo jirgin ne da misalin ƙarfe 10:12 na safiyar yau, agogon ƙasar Iran, ta hanyar amfani da wani sabon tsarin kariyar sararin samaniya da rundunar ta ce na zamani ne.

A cikin sanarwar, IRGC ta kuma ce wannan shi ne jirgin MQ-9 na Amurka na 53 da dakarun Iran suka yi ikirarin lalatawa.

Sai dai har yanzu wannan bayanin ya kasance da’awar rundunar IRGC, kuma ba a bayyana wata sanarwa mai zaman kanta da ta tabbatar da harbo jirgin ba.

Share Article:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

AMMASCO RADIO 90.7 FM is a leading broadcast station based in Kano, Nigeria. Founded as a corporate social responsibility initiative by Alhaji Mustapha Ado, a renowned business philanthropist and founder of AMMASCO Oil and Gas International Company.

Tags

Recent Post

  • All Post
  • GAME DA MU
  • LABARAI
  • SHIRYE-SHIRYE
  • TALLA
    •   Back
    • Labarai
    • Labaran Duniya
    • LABARAN KETARE
    • TSARO
    • KASUWANCI
    • NISHADI
    • LAFIYA
    • WASANNI
    •   Back
    • TUNTUBE MU

© 2025 Created with Royal Elementor Addons