Hukumar Tarayyar Turai ta gabatar da wani sabon ƙudiri da zai takaita yadda yara ke amfani da shafukan sada zumunta, a wani mataki da aka ce yana da nufin ƙara kare yara daga haɗurran intanet da kuma inganta lafiyarsu.
A ƙarƙashin sabon EU KIDS Act, yara ƙasa da shekara 13 ba za su samu damar amfani da shafukan sada zumunta ba. Sai dai za a iya ba su damar amfani da wasu dandamalin bidiyo da aka tsara musamman domin yara ta hanyar asusun da iyaye ko masu kula da su ke gudanarwa.
Yara masu shekaru 13 zuwa ƙasa da 15 za su iya amfani da abin da dokar ta kira “mini account”, wanda iyaye ko masu kula da su za su kafa tare da sa ido a kansa. Amfani da irin wannan asusun zai kasance da iyakokin wasu abubuwa, tare da iyakar awa ɗaya a rana.
Daga shekara 15, matasa za su iya buɗe da kuma sarrafa nasu asusun sada zumunta. Sai dai dandamalin za su kasance ƙarƙashin ƙa’idojin “safe by design”, waɗanda za su buƙaci samar da ƙarin kariya ga masu amfani da shekarunsu bai kai 18 ba.
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta ce tsarin zai mayar da nauyin tabbatar da tsaron yara kan kamfanonin fasahar sadarwa, ta yadda za su tabbatar da cewa ayyukansu sun dace da yara kuma suna da aminci.
Sabbin ƙa’idojin sun kuma shafi wasu abubuwa da ka iya jawo amfani da intanet fiye da kima, ciki har da infinite scrolling, wasu tsarin ba da lada da ke ƙarfafa ci gaba da amfani da manhajoji, da kuma sanarwar tura saƙonni a lokacin barci.
Hukumar Tarayyar Turai ta ce za a kuma ƙarfafa amfani da hanyoyin tantance shekarun masu amfani, tare da kare bayanan sirri yayin gudanar da wannan tantancewa.
An gabatar da EU KIDS Act a ranar 17 Satumba 2026, kuma har yanzu wannan tsari ne na doka da ke bukatar bin matakan amincewa kafin ya zama cikakkiyar dokar da za ta fara aiki a dukkan ƙasashen Tarayyar Turai.


