Ƴan sanda a Afirka ta Kudu sun tabbatar da gano gawar wata mace a yankin East Rand, lamarin da ya ƙara yawan gawawwakin mata da aka gano a yankin zuwa tara cikin watanni biyu.
Rahotanni sun ce an gano matar ne cikin mummunan yanayi, inda aka samu cewa an yanke mata maƙogwaro, yayin da wasu sassan jikinta ba su suturce ba.
Gano gawar ya ƙara tayar da hankali a yankunan Kempton Park da wasu wuraren da ke makwabtaka da shi, yayin da ake ci gaba da bincike kan jerin kisan matan.
A halin yanzu, ana yaɗa wasu jita-jita da ke alakanta kashe-kashen da wani mai kisan gilla da ke aiki shi kaɗai. Sai dai rundunar ‘yan sandan ta ce ba ta tabbatar da wannan alaƙa ba, kuma bincike na ci gaba da gano ainihin abin da ya faru.
Ya zuwa yanzu, iyalan mata uku ne kawai daga cikin waɗanda aka gano gawawwakin nasu suka samu damar tabbatar da cewa gawarwakin na ƴan’uwansu ne. Ana ci gaba da ƙoƙarin gano sauran waɗanda abin ya shafa.
Lamarin ya janyo fargaba tsakanin mazauna yankin tare da ƙara mayar da hankali kan matsalar cin zarafin mata da kashe mata a Afirka ta Kudu.
Hukumomi sun kuma ci gaba da jan hankalin mata da su kasance cikin taka-tsantsan, musamman wajen guje wa tafiya su kaɗai ko zama a wuraren da ba su da yawan jama’a, yayin da binciken ‘yan sanda ke ci gaba.


