Adadin mutanen da suka mutu bayan shan wani abin sha na gargajiya da ake zargin yana ɗauke da sinadarin guba a jihar Ondo ya ƙaru zuwa 49, yayin da kusan mutum 170 suka kamu ko kuma suka buƙaci kulawar lafiya, a cewar hukumomin jihar.
Lamarin ya fara bayyana ne a yankunan Araromi-Obu da Odigbo, da ke ƙaramar hukumar Odigbo, inda aka samu rahotannin mutuwar mutane bayan shan wani abin sha da ake kira “Monkey Tail”.
Da farko, Shugaban Ƙaramar Hukumar Odigbo, Taiwo Adegoroye, ya bayyana cewa mutane 24 ne suka mutu a Araromi-Obu da Odigbo. Daga baya adadin ya ƙaru zuwa 29, kafin ya kai 49 a ranar Laraba.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Ondo, Dr Banji Ajaka, ya ce lamarin ya kuma bazu zuwa ƙaramar hukumar Irele, inda aka samu ƙarin mace-mace.
Hukumomin lafiya sun ce alamomin da wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa suka nuna sun haɗa da matsanancin ciwon kai, rauni, matsalar gani, wahalar numfashi da kuma sauyin yanayin fahimta.
Sai dai hukumomi sun jaddada cewa har yanzu ana gudanar da gwaje-gwajen kimiyya domin tabbatar da ainihin sinadarin da ya haddasa mutuwar. An aika samfuran jini, fitsari da na abin sha da ake zargi zuwa dakunan gwaje-gwaje domin gudanar da binciken toxicology.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta kuma kama wani mutum mai suna Oloruntoba Babatunde, wanda aka fi sani da “Meko”, bisa zargin hannu wajen samar da wani ruwan gargajiya da ake zargi yana ɗauke da methanol. Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano alaƙar abin da aka kama da mace-macen.
Hukumomin jihar sun gargadi jama’a da su guji shan abubuwan sha na gargajiya ko na barasa waɗanda ba a tabbatar da ingancinsu ba, musamman daga wuraren da ba su da lasisi, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.


